Sunday, 11 March 2018

An daura auren mawaki Saeed Nagudu da masoyiyarshi da suka kwashe shekaru 7 suna soyayya

An daura auren fitaccen matashin mawaki kuma jarumin finafinan Hausa Sa'eed Yahaya Abubakar wanda aka fi sani da 'Sa'eed Nagudu'. Auren wanda aka daura shi a Asabar, hazikin matashin mawakin, ya auri sahibarsa ne A'isha Umar Na'iyachi  (Shatu) akan sadaki naira dubu hamsin, inda aka daura auren a Masallacin Murtala da ke unguwar Hausawa a cikin birnin Kano, da misalin karfe 11:00 na safe.Amarya da Angon daman dai sun dade suna soyayya tsakanin su wadda akalla sun fi shekara 7 a tare. Inda su ka yi alkawarin aure a tsakanin su sai daga baya kuma aka ga mawakin ya auri wata 'yar uwar sa a shekarar da ta gabata. inda har wasu suka rika tunanin ya yaudari A'isha. Ashe komai da lokacin sa.

Tun ranar Alhamis din da ta gabata ne aka soma gudanar da shagulgulan bikin, inda yau za a yi Friends day a Chicken Castle ranar 10th ga Maris

Walima a jiya Juma'a a Batul Event Center, Gandu Bayan Traid Fair, Kano

Sai kuma kamu a Gyadi-gyadi Court Road, a Bala Mamsa Street Dan Amar Close.

Wasu daga cikin 'yan fim da suka halarci bikin sun hada da Ali Nuhu, Usman Mu'azu, Kamal S. Alkali, Ali Gumzak, Garzali Miko, Sanusi Oscar, Alhaji Sheshe, Ali Ibrahim Dawayya, Ahmad Shanawa, Hassana da Hussaina da sauransu da dama.

Muna fatan Allah ya sanya alheri.
rariya.

No comments:

Post a Comment