Friday, 2 March 2018

An hana jiragen sama wucewa ta saman gidan Messi

Shugaban wani kamfanin sufurin jiragen sama dake turai, Vueling ya koka akan wata sabuwar doka da aka sa a filin sauka da tashin jirage dake Barcelona kusa da gidan tauraron dan kwallon kafa Lionel Messi, dokar dai ta hana jiragen sama wucewa ta saman gidan na messine.Gidan Messin dai yana canne wani gari dake gefen birnin Barcelonan, shugaban kamfanin jiragen, Sanchez Prieto ya bayyana cewa gaskiya wannan be kamata ba, yanzu jirage ba zasu iya bi ta kowane titi suke so ba saboda doka ta hanasu wucewa ta saman gidan Messi, ya kara da cewa babu inda ake irin wannan tsari a Duniya, kamar yanda kafar labarai ta Marca ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment