Saturday, 10 March 2018

An kara: Fatima Ganduje da mijinta Idris Ajimobi sun sumbaci juna a cigaba da shagalin bikinsu da ake yi a Oyo

An ci gaba da hidimar bikin 'ya'yan gwamnonin Kano da na Oyo, Fatima Abdullahi Ganduje da mijinta Idris Ajimobi a can jihar Oyo bayan da aka daura aure a Kano, manyan baki da suka hada da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da jigo a jam'iyyar APC, Bola Tinubu da uban amarya da uban Ango da sauran mawaka da masu nishadantarwa da 'yan uwa da abokan arziki sun halarci bikin.Kamar dai bikin da akayi a Kano da wani hoton masoyan biyu ya bayyana angon yana sumbatar amaryarshi wanda ya jawo cece-kuce, a wancan hoton mutane sunfi karfafa kushe ga hoton akan tunanin cewa ba'a daura aure ba lokacin da suka daukeshi.

A bikin Oyon ma anga wasu sabbin hotuna  ma'auratan suna sumbatar junansu.

Muna musu fatan Alheri da fatan Allah bada zaman lafiya.
No comments:

Post a Comment