Friday, 2 March 2018

An karrama Mansura Isah da lambar yabo saboda taimakawa marasa galihu

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa kuma mata a gurin Sani Musa Danja, Mansurah Isah ta samu lambar yabo da wata kungiya me zaman kanta ta bata akan taimakon da ta kewa marasa galihu, Mansurar ta nuna jin dadinta akan wannan kyauta sosai kuma ta bayyana cewa ita da sauran masu taimaka mata akan aikin da take yi zasu kara jajircewa akan aikin nasu.Muna tayata murna da fatan Allah ya saka mata da Alheri ya kuma kara daukaka.

No comments:

Post a Comment