Saturday, 17 March 2018

An kera mota ta farko a Duniya da kominta tsirara yake, kana kallonshi daga waje

A karin farko a tarihin Duniya an kera motar da, daga waje kana ganin komai na cikinta hatta injinta duk tsirara suke, wani kamfanin yin motane dake kasar Jamus ya kera wannan sabuwar mota a wani bajakolin sabbin motoci da akayi a kasar.Sannan kuma kamfanin ya bayyana cewa akwai na'urorin tsaro daban-daban na musamman da motar tazo dasu. To amma wasu na ganin cewa anya motarnan zata samu shiga gurin mutane kuwa?, dominfa ita mota kamar sirrice zaka yi ajiya, da kuma wasu abubuwan da baka bukatar wani ya gani a ciki.

Amma dai koma menene lokaci be bar komaiba.

No comments:

Post a Comment