Monday, 26 March 2018

An mika 'yan matan Dapchi hannun iyayensu

Gwamnatin Najeriya ta mika 'yan matan makarantar Dapchi 106 da kuma namiji daya a hannun iyayensu ranar Lahadi. Iyayen wasu daga cikin 'yan matan sun shaida wa BBC cewa sun tarbi 'ya'yan nasu cikin murna da annashuwa.


A cewar Malam Adamu Gashuwaram, 'yarsa ta isa gida cikin nutsuwa sabanin lokacin da mayakan Boko Haram suka mayar da su garin.

Mahaifiyar daya daga cikin 'yan matan ta gaya wa BBC cewa an tabbatar mata da zuwan 'yarta cikin garin amma tana jiran isarta gida.

"Gida ya cika da murna inda kowa ke dakon shigowarta," in ji ta.

Sai dai mahaifin Leah Sharibu, wacce ita kadai ce mai bin addinin Kirista da 'yan Boko Haram suka ki saki, ya ce suna cikin tashin hankalin rashin ganin 'yarsu har yanzu.

Ranar Asabar ne aka tabbatar wa Nathan Sharibu cewa a saki Leah kuma tana kan hanyar zuwa Dapchi domin saduwa da 'yan uwa da danginta.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment