Thursday, 15 March 2018

Ana cacar baki tsakanin shugaba Buhari da tsohon shugaba Jonathan: Bayan da shugaba Buhari ya zargi Jonathan din da nuna in kula lokacin aka sace 'yan matan Chibok

A ziyarar da yakai jihar Yobe jiya, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da sarakunan gargajiya, iyayen Al-umma da iyayen 'yan matan Dapchi da 'yan Boko Haram suka sace, shugaba Buhari ya shaida musu cewa tun bayan da aka sace 'yan matan Dapchin yana yin dukkan wani abu da ya kamata dan ganin cewa an maido da 'yan matan gida gurin iyayensu, shugaba Buhari yace yana samun labarin ya baiwa hukumomin tsaro da wani kwamiti na musamman da ya kafa umarnin su zo su duba yanda abin ya faru kuma su kawo mai rahoto cikin gaggawa.


Shugaba Buhari yace irin yanda ya dauki satar 'yan matan na Dapchi a muhimmanci ba irin yanda gwamnatin da ta gabata ta dauki satar 'yan matan Chibok bane, inda suka nuna halin ko inkula akai, wakilan gwamnatin tarayya tun daga tawagar da ministan labarai da al-adu, Lai Muhammad da kuma ta ministan cikin gida, Abdurrahman Dambazau sun kawo ziyara a garin na Dapchi dan ganin abinda ya faru da kuma daukar matakan da suka dace.

Haka shugaba Buhari yace irin muhimmancin da suke baiwa irin wannan lamari yasa suka kwato 'yan matan Chibok har guda dari daga hannun Boko Haram dan haka suma ya tabbatar musu dacewa za'a dawowa da iyayen 'yan matan 'ya'yansu.

To saidai a wani martani da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya mayar wa shugaba Buharin yace ba gaskiya bane wai ace lokacinshi be dauki satar 'yan matan Chibok da muhimmanci ba, yace bayan da yaji labarin satar 'yan matan nan da nan ya kira taron manyan jami'an tsaro na kasa dan a samo hanyar da za'a magance wannan matsala kuma cikin kankanin lokaci jami'an soji suka bazama neman 'yan matan chibok din. Yace har yanzu shugaba Buhari be gudanar da taron jami'an tsaro na kasa ba akan satar 'yan matan Dapchi saboda haka shine be dauki wannan labari da muhimmanciba, hasalimai akwai muhimmin taron da ya kamata shugaba Buharin yayi bayan satar 'yan matan Dapchi din amma ya dakatar da taron ya tafi wani taron tattalin arziki.

Haka kuma lokacin da danshi, Yusuf yayi hadarin babur haka ya dakatar da komai ya garzaya Asibitin da aka kwantar dashi amma a lokacin da aka sace 'yan matan Dapchi sai ga shugaba Buharin ya tafi Kano gurin biki inda yaje suka sha shagali a lokacin da ake kashe-kashe a jihohin Zamfara, Benue, Taraba da sauransu, dan haka shine be dauki maganar tsaro da muhimmanci ba.

Jonathan ya kara da cewa kuma wai da Buharin yace cewa sun kwato 'yan matan Chibok daga gurin Boko Haram ba haka abin yake ba, 'yan Boko Haram ne da kansu suka saki 'yan matan Chibok din bayan da aka basu makudan kudin fansa, wa ya sani ma watakila da wannan kudinne suka yi amfani suka sake sayan kayan aikin da suka sace 'yan matan Dapchi?

Ya kara da cewa a kwanan nan wani jami'in 'yan sanda ya fito ya fadi cewa waki jami'an 'yansanda dubu dari da hamsin dake gadin 'yan 'yan siyasa, me zaisa Buhari bazai kwashi wadannan jami'an 'yan sanda ba wajan sakasu inda ya dace dan kawo tsaroba.

Jonathan ya kara da cewa karfa 'yan Najeriya su manta a lokacin da ya ke daukar matakin da ya dace akan 'yan Boko Haram Buhari cewa yayi a wancan lokacin matakin soja da aka dauka hari ne da kuma cin zarafi kan mutanen Arewa.

Dan haka Shi bai dauki maganar satar 'yan matan Chibok sakwa-sakwa ba a lokacinshi, Buharinne ya dauki maganar satar 'yan matan dapchi sakwa-sakwa.

Vanguard.

No comments:

Post a Comment