Monday, 12 March 2018

'Anya Fatima Ganduje ba kwaya tasha ba kamin ta tika wannan rawar'?

Har yanzu wasu sabbin hotunan shagalin bikin 'ya'yan gwamnonin jihahohin Kano da na Oyo sai kara fitowa suke, mutane na ta kara bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan wadannan hotunan da kuma bidiyon da Fatimar tayi rawa.A wani bidiyo da tauraruwar fina-finan Hausa, Saratu Gidado, Daso ta saka a dandalinta na sada zumunta da muhawara inda ta bayyana cewa ita rawar Fatimar ta birgeta, wasu sunce gaskiya suna tsammanin Fatimar ba cikin hayyacinta tayi wannan rawar da tayi ba, watakila dai tasha kwayane, amma Daso ta kare ta da cewa babu abinda ta sha, farinciki ne kawai.

No comments:

Post a Comment