Monday, 26 March 2018

Arsenal ta dauki sabon Coach da zai maye Arsene Wenger

Wasu rade-radi dake fitowa daga kungiyar Arsenal na cewa kungiyar ta fara tattaunawa da wani sabon kocin da zai maye gurbin Arsene Wenger, kocin da ake sa ran zai maye Wengern shine tsohon kocin kungiyar Borussian Dortmund, Thomas Tuchel.


Kungiyar Bayern Munchen sun so su daukeshi aiki amma ya bayyana musu cewa Ingila zai koma da aiki kuma ana sa ran Arsenal dinne zasu daukeshi.

Saidai Wenger ya bayyana cewa ana nunamai kiyayyane kawai a Arsenal din saboda tsufanshi amma dai duk hukuncin da aka yanke a kanshi zai karba, kamar yanda Eurosport suka ruwaito.

No comments:

Post a Comment