Saturday, 3 March 2018

'Ashe haka aure ya ke da arha a kasar Hausa?: To gaskiya a karawa dana mata daya'>>Inji Gwamna Ajimobi bayan da Gwamna Ganduje yace mai dubu 50 ne kudin sadakin diyarshi

Me baiwa gwamnan jihar Kano shawara akan sabbin kafofin watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai ya hada wani abin barkwanci inda ya saka wannan hoton yace wai lokacin da gwamna Ganduje ne ya gayawa Gwamna Ajimobi cewa dubu hamsinne Sadakin diyarshi, shine Ajimobin ya bude baki cikin mamaki, yace ashe haka aure ke da arha a kasar Hausa?


To indai hakane a karawa danshi, mata daya.

Hmmmm watau za'awa Fatima Kishiya tun kamin ta shiga kenan.

No comments:

Post a Comment