Wednesday, 21 March 2018

Ba a biya kudin fansa ba kamin Boko Haram su saki 'yan matan Dapchi: Sune da kansu suka ga rashin dacewar abinda sukayi suka dawo da 'yanmatan>>Lai Muhammad

A yaune mayakan Boko Haram suka dawo da 'yan matan makarantar Dapchi da suka sace su dari da hudu da hadin wani yaro da kuma yarinya, wanda hakan yakai yawan wadanda aka dawo dasu din dari da shida kamar yanda gwamnatin tarayya ta bayyana, da yake magana da manema labarai, ministan labarai da al-adu Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa ko sisi gwamnati bata biya ba akan sakin 'yan matan haka kuma ba musayar wasu mayakan na Boko Haram  da gwamnati ke tsare da su ba akayi kamin su saki yaran ba.Ya kara da cewa sune da kansu sukaga rashin dacewar hakan suka dawo da 'yan matan domin hakan ya sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta da akayi da mayakan na Boko Haram.

Tuni dai har jami'an tsaro sun mikawa tawagar da shugaban kasa ya aika jihar Borno data hada da Ministan labarai da al-adun, Lai Muhammad da kuma ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau da kuma karamar ministar harkokin waje Khadija 'yan matan a barikin sojojin sama dake Maidugurin.

No comments:

Post a Comment