Thursday, 15 March 2018

'Ba sulhu nike nema da Ali Nuhu ba amma bana kin sulhu'>>Bello Muhammad Bello

A kwanakin baya kadanne aka samu fadan cacar baki tsakanin yaran jaruman fina-finan Hausa wanda suka hada da Ali Nuhu da Adam A. Zango da Bello Muhammad Bello, wasu jaruman sun goyi bayan wasu yayin da wasu suka yi shiru, andai sasanta Ali Nuhu da Adam A. Zango amma ta bangaren Bello abin ya dan cigaba har zuwa wani lokaci.Tun bayan wacan lamari kusan za'a iya cewa babu wani abu na zahiri da ya hada Ali Nuhun da Bello, to amma jiya yayin da Ali Nuhun ke murnar cika shekaru goma sha biyar da yin aure, Bellon ya saka hotunan lokacin da ya halarci daurin auren Alin, shekaru sha biyar da suka gabata. Haka kuma ya saka hotunan lokacin da Ali Nuhun shima ya halarci daurin aurenshi inda yace Alin ya ramawa kura aniyarta.

Bellon dai yace ba sulhu yake nema ba ba kuma sulhu yake kiba.

Haka kuma a yauma da Alin ke murnar zagayowar ranar haihuwarshi Bellon ya saka hotunansu lokacin dangantakarsu batayi tsami ba kuma ya tayashi murna amma yace ba sai Alin ya amsa ba dan shi dan Allah yayi.

"Cikin ikon ALLAH (SAW) yau shekaru goma sha biyar kenan dani ta tawagata a wajen bikin auren Ali Nuhu.
TAMBAYAR ITACE: SU KANANAN MUNAFUKAN SUNA INA SHEKARU 15 DA SUKA WUCE?
Hoto na biyu kuma, Ali Nuhu ne a wajen bikin aurena shekara daya da ya wuce inda shima ya ramawa kura aniyarta.
BA SULHU NAKE NEMA BA, BA SULHU NAKE QI BA. Saboda Manzon ALLAH ma bai guji sulhu ba.
KAWAI DAI TUNATARWA NE GA MUNAFUKAI.
ALLAH ya shiryar damu tafarki madaidaici."

No comments:

Post a Comment