Thursday, 15 March 2018

'Ba tsoron Ali Nuhu yasa na tayashi muranar zagayowar ranar haihuwarshi ba'>>Bello Muhammad Bello

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB ya bayyana cewa shifa ba tsoron Ali Nuhu yasa ya tayashi murnar zagayowar ranar haihuwarshi ba, baya tsoron kowa sai Allah kuma be taba rokon wani dan su sasantaba banda mahaifanshi, a yaune dai Ali Nuhu, sarki yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi kuma Bellon ya tayashi murna inda har ya fadi cewa ba sai Alin ya amsashi saboda shi dan Allah yayi.


Amma da yammannan sai ga Bellon ya fito yana magana akan wasu da suke cemai wai tsoron Aline yasashi ya tayashi murnar zagayowar ranar haihuwarshi kuma har yasha alwashin zaiyi maganinsu.

Amma mutane da dama ciki hadda Ummi Zeezee sun bashi baki akan kada ya biye musu kuma yaji wannan kira da aka mishi inda ya fito yace komai ya wuce.

Tun bayan da akayi fadan cacarbaki tsakanin Bellon da yaran Ali Nuhu wanda Bellon ya zargi cewa Alin ne ya turosu su mai rashin kunya da alama dangantaka tayi tsami tsakaninsu.

Muna fatan Allah yasa a sasanta.

No comments:

Post a Comment