Wednesday, 28 March 2018

'Ba'a fahimci T.Y Danjuma ba a maganar da yayi ta cewa mutane su kare kansu'>>Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya kare abinda tsohon ministan tsaro, T. Y Danjuma ya fada na cewa mutane su tashi su kare kansu daga masu kai musu hare-hare, Ortom yace ba'a fahimci Danjuma bane, bawai yana nufin mutane su rike makamai ba, amma kowa yasan cewa kariyar kai tana bisa doka, babu wanda zai zauna a gidanshi yana ganin mugu yazo ya cutar dashi.


DailyTrust ta ruwaito cewa  gwamna Ortom ya bayyana cewa bawai saida bindiga mutum zai kare kanshiba, akwai hanyoyi da dama da za'a iya amfani dasu wajan kariyar kai.

No comments:

Post a Comment