Monday, 19 March 2018

Babu kama ta: Na zarce kowa a Duniyar kwallo>>Ronaldo

Tauraron dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa babu kamarshi, babu wanda za'a iya hadashi dashi a Duniyar kwallo saboda bega wani dan kwallon da ya kaishi jajircewa da kwazo da iyawaba.


Cristiano Ronaldo yace babu wanda zai taba zama kamarshi, mutum zai yi iya yinshi amma bazai taba zama Criatiano Ronaldo ba domin shi na dabanne, Cristiano Ronaldo ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda yake sanye da wasu sabbin kayan kamfanin NIKE.

Ronaldo dai wanda ya fara haskakawa a kungiyar Manchester United a shekarar 2003 ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Ballon D'or ta farko a can a shekarar 2008 kamin daga baya yazo Kungiyar Real Madrid inda ya lashe kayutar sau hudu, dama duk wata kyauta da ko wane dan kwallo yake hankoron samu.

Ana dai hada Ronaldo ne da abokin takararshi na Barcelona, watau Messi amma masu sharhi na ganin Messi kwalllonshi ta baiwace, shi kuwa Ronaldo dagiyace da jajircewa da naci tasa yace haskakawa.

Ronaldon ya kara da cewa tun yana Manchester ya gayawa kanshi cewa sai ya zamo tauraron dan kwallon Duniya da babu irinshi.

No comments:

Post a Comment