Thursday, 29 March 2018

'Babu wutar Jahannama'>>inji Paparoma Francis

Shugaban kiristoci, Paparoma Francis yayi bayanin cewa wai babu wutar Jahannama da Allah zai hukunta wadanda suka kafircemai, wannan batu nashi ya matukar dauki hankulan Duniya, hatta kiristoci da yawa sun barranta da wannan jawabi na paparoma, yayi wannan magane a wata hira da akayi dashi a wata jaridar kasar Italiya.


Paparoma ya bayyana cewa, idan mutane suka mutu, wanda yabi Allah za'a sakashi a Aljanna wanda kuma yake da zunubi, yaki bin Allah to ba wuta za'a sakashi ba, kawai zai bace ne yabi Iska.

Subhanallah.

No comments:

Post a Comment