Thursday, 8 March 2018

'Banga dalilin hada abinda Rahama Sadau tayi da wanda diyar Ganduje tayi ba: Nasan ka na da abinyi: Ka dena bata datarka a banza'>>General BMB ya gayawa T. Y Shaban

Baya ga masoya na waje dake sukar tauraron fina-finan Hausa T. Y Shaban akan alakanta abinda Rahama Sadau tayi da wanda diyar gwamnan jihar Kano tayi da mijinta da kuma sukar abokin aikinshi Nura Hussain, Shaban ya fara samun suka daga cikin abokan aikinshi inda tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB ya bashi shawarar cewa shi baiga dalilin hada abinda Rahama Sadau tayi ba da wanda diyar Ganduje tayi ba.


BMB ya kara da cewa abinda Rahama Sadau tayi ya wuce kamata yayi abarshi yawuce a barta taji da sana'arta haka kuma itama diyar gwamnan Kano, Fatima kamata yayi a barta taji da rayiwar aurenta.

BMB ya kuma kara da cewa yasan T. Y Shaban din na da abinyi wanda yafi wannan magana ta hotunan auren diyar gwamnan Kano, to be kamata yana lalata da datarshi a banzaba.

Haka kuma BMB din yayi doguwar Nasiha akan wannan batu inda yace ba'a shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa kuma kowa nada nashi zunubin.

Gadai abubuwan da ya fada kamar haka:

"Da dai banyi niyyar cewa komai ba amma yanzu bari na dan tofa albarkacin bakina. NI A GANI NA RAYUWA JARRABAWA CE, KOWA NADA QUESTION PAPER DINSHI, KUMA BABU MA'ASUMI SAI ANNABI MUHAMMADU (SAW) MAI KAZA A ALJIHU DAI BAYA JIMIRIN ASSS! KOWA NADA IRIN NASHI LAIFIN, MAFI MUNI MA SHINE ABUBUWAN DA WASU KEYI A BOYE SUNA GANIN BA MAI KALLON SU, SUN MANTA DA CEWA ANNABI MUHAMMADU (SAW) "An ta'buda allaha ka annaka tarahu, fa in lam takun tarahu, fa innahu yaraka" "Ka bauta wa ALLAH kamar kana ganinshi, idan kai baka ganinshi, Shi yana ganinka" Dukkanmu masu laifi, duk da cewa kowa irin laifin shi, na wani yafi na wani muni, idan har mun yarda da haka, to ya zama dole mu yarda cewa laifi tudu ne, sai mun hau kan namu sannan mu dinga hango na wasu. Iya ruwa dai fidda kai, kuma yada laifi ma laifi ne, maimaita sabo sabo ne, tozarta bawa laifi ne. Ku bar Fatima Ganduje da mijinta, ku bar Rahama Sadau, kuji da kanku kawai, kuyi fatan gamawa da duniya lafiya, ba'a shiga tsakanin bawa da ALLAH. Akwai hadisin dake cewa "Zaka ga bawa yana aikata aiki irin na 'yanwuta, amma idan ALLAH ya so kafin mutuwarshi, sai kaga ya koma aikata aiki irinta 'yan Aljanna, kuma sai ya shigeta. Za kaga wani bawa yana aikata aiki irinta 'yan Aljannah, gabannin mutuwarshi, sai ya baude, sai kaga ya shiga wuta" Daga karshe ga wata nasiya daga Annabi Muhammadu “Man kaana yu'minu billahi wal yawmil aakhiri fal yaqul khairan aw liyasmut" "Duk wanda yayi imani da ALLAH da kuma ranar karshe, to ya fadi alkhairi ko yayi shiru" "Whoever believes in ALLAH (SWT) should speak what is good or remain silent" ALLAH YA SA IDAN LOKACINMU YAYI, MUYI KYAKKYAWAN KARSHE."


No comments:

Post a Comment