Thursday, 15 March 2018

Barcelona, Messi sun kafa tarihi: Wata kila hukumar shirya wasan cin kofin zakarun turai su hukunta Barcelonar

A wasan cin kofin zakarun turai da Barcelona ta buga da Chelsea jiya, Laraba, kungiyar ta kafa tarihi inda nasarar da tayi jiya ta bata damar zuwa matakin wasan kusa dana kusa dana karshe sau goma sha daya kenan a jere tun daga shekarar 2007. Haka shima Messi yaci kwallayenshi na casa'in da tara da kuma na dari a wasan na jiya da ya zura kwallaye biyu.


Messin dai ya kuma kafa tarihin cin kwallo cikin mafi kankanin lokaci a tarihin buga kwallonshi inda ya zura kwallon a sakwanni dari da shirin da tara da fara wasa.

Bayan kammala wasan na jiya an samu rahotannin cin zarafin wasu magoya bayan Chelsea da akayi a filin wasan na Barcelona kuma me magana da yawun Chelsean ya bukaci duk wani masoyinsu da aka ci zarafinshi ya fito ya bayyana musu zasu kaiwa hukumar dake shirya wasan na zakarun turai dan a hukunta Barcelonar.

No comments:

Post a Comment