Friday, 9 March 2018

Barcelona na tsoron cewa Messi zai iya canja kungiyar kwallon kafa akan kudi mafi tsada da a Duniya

Kungiyar Barcelona na daridarin cewa tauraron dan kwallonsu Lionel Messi zai iya komawa wata kungiyar kwallon kafa idan sukayi sake, me kula da harkar kudade da tsare-tsare na kungiyar Schroda ne ya bayyanawa kafar Skysport haka a wata zantawa da yayi dasu.


Ya bayyana cewa duk da yake Messin a shekarar data gabata ya sanya hannu akan kwantirakin tsayawa a kungiyar har zuwa shekarar 2021, kuma a wancan lokacin yana da damar komawa wata kungiyar amma ya jaddada kaunarshi ga Barcelona, sannan kuma suma kungiyar dan su tabbata cewa babu wata kungiya da zata  iya kawo harin siyanshi suka saka tsabar kudi har Euro miliyan dari bakwai akan cewa duk kungiyar da zata sayi messin zata biya, amma yanzu suna ganin cewa yanda abubuwa ke canjawa za'a iya samun wata kungiya ta biya wadannan damman kudin dan sayen Messin.

Schroda yace, abinda ya faru kenan lokacin Neymar, suka saka mai kudi har Euro Miliyan dari biyu da ashirin da biyu dan su tabbata cewa ya zauna a kungiyar tasu har tsawon lokacin da zaiyi ritaya daga kwallo amma sai gashi an samu PSG ta biya wadannan kudi.

Schroda yace gaskiya zasu sake tunanin kara yawan kudin da suka sawa Messi domin ga dukkan alamu idan suka barsu a haka wata kungiya zata iya zuwa ta sayeshi a haka, a barsu da buda baki.

No comments:

Post a Comment