Saturday, 24 March 2018

Boko Haram Sun Sako Dalibar Dapchi Da Suka Rike Saboda Ta Ki Karbar Musulunci

Kungiyar Boko Haram ta sako sauran yarinya daya tilo da ta rage a hannunta daga cikin ‘Yan matan sakandiren Dapchi da suka dawo da su, inda rahotanni ke nuni da cewa yanzu haka tana kan hanyarta ta dawowa gida.


A baya dai Boko Haram ta yi ikirarin cewa ba za ta saki Leah Sharibu ba har sai ta karbi addinin Islama.

Mahaifin Leah Sharibu Nathan ya bada tabbacin cewa Boko Haram ta sanar masa da cewa ‘yar tasa za ta dawo gida a yau Asabar kamar sauran rakwarorinta ‘yan matan na Dapchi.

No comments:

Post a Comment