Monday, 5 March 2018

Buhari Na Da Damar Zuwa Inda Ya Ga Dama, Martanin Fadar Shugaban Kasa Ga Masu Sukar Shugaba Buhari Akan Daurin Auren 'Yar Ganduje Da Ya Halarta A Kano

Babbar mataimakiyar shugaba Muhammadu Buhari akan kafar yada labarai na zamani, Lauretta Onochie ce ta fito take kare Ubangidan nata akan daurin auren 'yar gidan gwamna Ganduje da ya je a garin Kano wanda ya janyo cece-kuce a kafafen sadar da zumunta na zamani. Inda wasu suke ganin halartar daurin auren bai dace ba, kamata ya yi a ce shugaban kasan ya kai ziyara wurare da dama da ake fuskantar matsaloli kamar jihar Yobe da aka sace 'yan makaranta a garin Dapchi amma sai ya ya bige da halartar taron biki.


Da take mayar da martani ga wadanda suke sukar a shafinta na twitter, ta bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ba yaro bane, mutum ne mai cikakken hankali saboda haka yana da damar yanke hukuncin inda zai tafi.

Onochie tace: "shugaba Muhammadu Buhari ba yaro bane, cikakken mutum ne wanda ya mallaki hankalin kansa. Saboda haka yana da damar ya yanke hukuncin inda zai tafi ziyara. Kuma ya yanke shawarar zuwa Kano, saboda haka kuma ya tafi"

Shidai bikin na 'yar gidan gwamna Dandujen da dan gidan gwamna Abiola Ajimobi na Oyo wanda ya gudana a Kano a ranar Asabar din da ta gabata,ya samu halartar shugaba Muhammadu Buhari tare da rakiyar gwamnoni 22 daga jihohin kasar nan.

Haka kuma bikin ya samu halartar shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da kuma jagoran jam'iyar APC na kasa.

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose yana daga cikin wadanda suka caccaki shugaba Buhari akan halartar bikin, inda a cewar sa kamata ya yi a ce ya damu da abubuwan alhinin da suka faru a sassa daban-daban na kasar nan musamman arewacin Nijeriya, ba taron biki ba.
rariya.

No comments:

Post a Comment