Tuesday, 13 March 2018

Cin Haram Din Da Ake Yi A Majalisa Ya Yi Yawa, Shi Ya Sa Na Bayyana Badakalar Naira Milyan 13.5 Da Ake Baiwa Sanatoci>>Sanata Shehu Sani

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisan dattawa, Shehu Sani ya bayyanawa duniya cewa shi da abokan aikinsa sukan amshi N13.5 million a wata domin ayyukan jin dadinsu sabanin albashin da suke samu.


Ya ce "na yanke shawaran bayyanawa ne saboda kare mutunci".

Ya ce ana gudanar da majalisar dokokin tarayya cikin rashin gaskiya kan yadda ake kashe kudade. Don haka yana son a daina biyan Sanatoci kudin haram saboda marasa aikin yi su daina takara a zaben majalisa kowace shekarar zabe.

"Majalisar dokokin tarayya na daga cikin ma’aikatun gwamnati wadda rashin gaskiya ya fi yawa. Na duba al’amarin sai naga ya kamata in bayyanawa duniya kowa ya ji ya gani abin da muke amsa. Idan aka daina biyan wadannan kudade, wadanda ba su da manufa na kwarai za su daina zuwa majalisa", cewar Sanata Shehu Sani.
Rariya.

No comments:

Post a Comment