Monday, 19 March 2018

Cristiano Ronaldo yaci kwallaye uku a wasa daya(Hat-trick) sau 50

Tauraron dan kwallon kafa me bugawa kungiyar Real Madrid wasa, Cristiano Ronaldo ya ci kwallye sau uku a wasa daya sau hamsin kenan wanda ake kira da Hat-trick a turance, dan shekara talatin da uku ya kai ga wannan matsayine bayan yaci kwallaye hudu a wasan da Madrid din ta buga jiya, Lahadi da Girona wanda aka tashi Madrid tayi nasara da ci 6-3.


Ronaldo dai yaci kwallaye sau uku a wasa daya sau arba'in da hudu a Real Madrid sannan kuma yaci sau biyar a kasarshi ta Portugal sannan kuma yaci sau daya a tsohuwar kungiyarshi ta Manchester United.

No comments:

Post a Comment