Tuesday, 13 March 2018

DA MUN SAN ZA A YI BADALA A GURIN AUREN 'YAR GANDUJE DA MUN TURA JAMI'ANMU SUN YI KAME A GURIN>>INJI HUKUMAR HISBAH TA KANO

Mataimakin kwamadan rundunar 'yan Hisbah ta jihar Kano Dr Yakubu Maigida Kachako  ya bayyana cewa da sun san cewa za a aikata badala da masha'a a gurin bikin 'yar gwanan Kano da sun tura jami'an su na Hisbah sun yi kame a gurin saboda gwamnatin jihar Kano ta ba su damar su yi aiki a ko ina, kuma gwamnatin tana ba su hadin kai akan ayyukansu.


Dakta Kachako ya ci gaba da cewa shi kanshi gwamnan bai san za a aikata badala ba a gurin da ba zai bari hakan ta faru ba.

Dakta Maigida Kachako ya yi wannan jawabin ne a yayin zantawar su da 'yan jaridu a shelkwatar hukumar Hisba dake birnin Kano.
Rariya.

No comments:

Post a Comment