Wednesday, 21 March 2018

'Da na jira sai an kaini kotu amma yanzu zan bayyana hoton bidiyon hujjata akan Maganar 'yan Luwadi da nayi: Bana magana babu hujja >>General BMB

A dazu ne mukaji labarin cewa, tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB yayi zargin wani da yin Luwadi duk da be kira suna ba amma yayi habaici, inda yake cewa ba za'a kara yi a Jos ba saidai a tafi can, a wancan lokacin Bello yace yana so idan wadanda yawa maganar sunji Haushi su kaishi kotu shi kuma a lokacinne zai bayyanawa Duniya hujjojinshi, to amma yanzu yace an kusa kaishi bango, allura zata tono Garma ba ma sai anje kotu ba yana da hujjoji har guda uku kwarara.Bello ya kara da cewa baya muna furci kuma daga cikin hujjojin da zai bayyana na bidiyo hadda wanda abin ya faru dashi kuma ya zabi yaji kunyar Duniya maimakon ta lahira, ya fito ya bayyana abinda ya faru.

Bello dai yace a jirashi nan da dan wani lokaci, a koda yaushe zai iya sakin hotunan bidiyon.

Ga abinda yace kamar haka:
"

ALLAH KA CETO BAYINKA DAGA HANNUN WADANDA SUKA BATA TUN KAFIN SUYI NISA.
Idan ni kadai zan rage mai fadin gaskiya, wallahi, zagi daga nesa, jifa, yarfe, tsafi, dauri ba za su iya dakatar dani ba.
Hirarmu da Actor na film din sakata, Bashir
Idris Baba Otu da nayi niyyar daurawa, aka yimin nasiha, nace na bari, daga baya kuma karnuka suka cigaba da haushi. Yanzu anzo gurin!
Duk wanda ke Jos ko yasan Jarumin Sakata yasan komai sai dai kin ALLAH ya hana shi fadin gaskiya.
ALLAH KARA MANA KARFIN GWIWAN FADIN GASKIYA KODA A BAKIN ARMOUR TANK MUKE.
DA ALLAH NA DOGARA!!!"

"Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Akwai hujjoji uku wasu daga bakin wadanda suka zabi
su fadi gaskiya suji kunyar duniya da suyi
shiru suji kunyar lahira."


No comments:

Post a Comment