Tuesday, 6 March 2018

Dalilin da ya sa bana gaggawar ziyarar guraren da wani abu ya faru

A ziyarar da ya kai jihar Taraba, jiya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilinshi na rashin kai ziyara cikin gaggawa jihohin da rikice-rikice suka shafa, yace yana da hanyar da yake bi yasan duk wani abu dake faruwa a cikin kasarnan ta hanyar samun rahotannin sirri.Inda daga baya kuma sai ya kai ziyara.

Yayi kira da cewa duk wani bafulatani da aka gani da bindiga a kaishi kotu, ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da su yiwa mutanensu hudubar son juna da zaman lafiya domin sune sukafi kusa da jama'a kuma mulkinsu na tsawon lokacine wanda har saisun mutu amma shi Buharin da gwamna Ishiaku na dan lokacine dan saboda fadace-fadace da kashe-kashe babu inda zai kai kasarnan.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa dalilin zabar  jihar Taraba a matsayin ta farko a cikin jerin jihohin da zai kaiwa ziyara shine, yawan mutane da aka kashe a jihar yafi yawan wadanda aka kashe a jihohin Zamfara da Benue.

A karshe shugaba Buharin ya bayyana cewa idan ya dawo daga kasar Ghana zai kai irin wannan ziyara ta jajintawa mutanen jihohin Zamfara, Benue, Rivers da Yobe.

No comments:

Post a Comment