Monday, 19 March 2018

Dalilin da ya sa na jinkirta bayyana tsayawa takara

A wata hira da akayi da me magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya so ya bayyana aniyarshi ta tsayawa takara a shekarar 2019 idan Allah ya kaimu saboda kada 'yan adawa su canja mai ra'ayi.


Ya kara da cewa yanzu kusan shekara daya kenan kamin zaben idan shugaban kasa ya fito yace zai tsaya takara to 'yan adawa na iya amfani da wasu lamurra dake faruwa a kasarnan su sanyawa Buharin kahon zuka har watakila susa yace ya fasa, shiyasa ya jinkirta bayyana tsayawarshi takara sai can gaba lokacin da ya dace, kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment