Saturday, 31 March 2018

Daukar hotunan da shugaba Buhari yayi da wata tauraruwar kasar Ingila ya jawo ce-ce kuce

A lokacin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke ziyara a jihar Legas, yaje kaddamar da katafaren tagwayen gine-ginen benayen da akeyi akan ruwa a jihar da ake kira da Eko Atlantic City, shugaba Buhari ya dauki hotuna da wata tauraruwar fina-finan kasar Ingila da ta kawo ziyara Najeriya me suna Naomi Campbell.


Bayan daukar hotunan, Naomi taje dandalinta na sada zumunta inda ta bayyana cewa shugaba Buharin ya gayyaceta wajan bude wannan guri a jihar Legas, amm sai fadar shugaban kasar ta hannun me baiwa shugaba Buharin shawara tafannin sabbin kafafen watsa labarai ya karyata wannan ikirari nata inda yace, ita Naomi dince akayi sa'a lokacin da shugaba Buhari yake rangadin gurin itama tazo gurin shine ta nemi a bata damar daukar hoto dashi amma ba gayyatarta yayi ba.
Ai kuwa sai gashi Naomi ta canja wannan labari nata zuwa cewa ta gamune da shugaba Buharin a wajan kaddamar da wancan aiki, amma asalin abinda ya kawota Najeriya, ta zo ne halartar wani taron nuna kawa da za'ayi.

Wannan batu ya matukar dauki hankulan 'yan Najeriya inda akayi ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi  akai, yayin da wasu ke ganin mayar mata da martanin da fadar shugaban kasar tayi be kamataba, domin kamar an kunyatatane, wasu kuwa sun goyi bayan hakan.


No comments:

Post a Comment