Thursday, 22 March 2018

Daya daga cikin 'yan matan Dapchi ta bayyana yanda Boko Haram suka sace su da inda suka kaisu

Daya daga cikin 'yan matan ta shaida wa BBC yadda aka sace su:

"Muna zaune a cikin dakunanmu sai muka ji kara, da farko mun dauka cewa na'urar raba wutar lantarki ce ta fashe, sai muka ji karar ta ci gaba.


Sai suka shigo dakananmu, inda muka yi kokarin ficewa ta kofar baya amma sai suka sha kanmu suka zuba mu motoci.

A kan hanyar tafiya ne biyar daga cikinmu suka mutu.
Daga nan sai suka kaimu wani wuri inda muka kwana sannan suka sa muka dafa abinci muka ci.

Sai suka kara tafiya da mu wani wurin daban.

Sun rinka kula da mu suna ba mu abinci da ruwan sha, ba su yi mana komai ba".
Da aka tambaye ta ko za ta koma makaranta sai ta ce:

"A'a. Sun shaida mana cewa ka da mu ci gaba da karatun boko".

No comments:

Post a Comment