Saturday, 31 March 2018

Dino Melaye zai fitar da sabon kundin wakoki

Dan majalisar dattawan Najeriya Dino Melaye ya ce nan ba da jimawa ba zai fitar da sabon kundin wakoki. Sanatan ya shaida wa BBC cewa "kowa yana da baiwar da Allah ya yi masa. Ni Allah ya min baiwar waka, da a ce na je na zage ka gara na yi maka gwalo. Saboda haka ina son waka. In Shallau kwanan nan zan fitar da sabon kundin waka."


A cewarsa, yana matukar son hawa motoci na kece-raini saboda suna burge shi.

Da yake bayar da amsa kan zargin da ake yi masa na gudanar da rayuwa harholiya, Sanata Dino ya ce "Duk wanda ya ce ba zan ji dadin rayuwata ba karya yake yi; zan rika sa kaya masu kyau, zan hau motoci masu kyau, amma ba zan yi sata ba kuma tun kafin na zama sanata nake hawa motoci. Tun da na zama sanata ban sake sayen sabbin motoci ba".
bbchausa.

No comments:

Post a Comment