Monday, 5 March 2018

'(Diyar Ganduje) ta jawo mana maganganu wallahi: Da dan fim ne yayi haka da kaji dirar ayoyi'


Bayan da hoton, Fatima Abdullahi Ganduje, diyar gwamnan Kano ya bayyana mijinta, Idris Ajimobi na sumbatarta a shafukan sada zumunta da muhawara, mutane sun yi ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. 'Yan fim din Hausa ma ba'a barsu a bayaba, tauraron fim din Hausa kuma me gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin, T. Y Shaban ya bayyana cewa da 'yan fim ne sukayi irin wannnan abu to da kaji dirar ayoyi.Bayan da Shaban ya saka hoton a dandalinshi na sada zumunta, abokin aikinshi, Iliyas Tantiri yace, duk da aurene amma gaskiya bai dace ba wannan daukar hoton da sukayi domin inaga ko tarbiyya musulunci bata zo da haka ba. Wannan yarinya ta ja mana maganganu wallahi.

Shaban kuma ya bashi amsa da cewa, Matsalar rashin adalci a tsakaninmu a zamantakewa....da 'yanfim ne da kaji dirar ayoyi.


No comments:

Post a Comment