Saturday, 17 March 2018

'Diyata na so ta gaji sarautata'>>Sarkin Kano

A wata hira da yayi da jaridar Financial Times, me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ya bayyana cewa daya daga cikin 'ya'yanshi mata naso ta gajeshi a matsayin sarauniyar Kano kuma tana ta matsamai lamba akan rashin saka mace cikin mayan masu bashi shawara na fadar.


Sarki Sanusi be bayana ko wacece daga cikin 'ya'yan nashi ba ke so ta gajeshi amma a kwanakin baya sarkin ya taba tura diyarshi Shahida wani taro da akayi akan satar 'yan matan Chibok inda ta wakilceshi, abinda ya jawo cece-kuce a wancan lokacin saboda bataje da hijabiba sai gyale kuma wancan lokacin shine karo na farko da mace ta taba wakiltar sarki a gurin taro.

Dama dai sarkin na Kano ya taba bayyana cewa ga masu ganin cewa ya cika tsauri akan abubuwa to 'ya'yanshi sun fishi tsauri da kokarin ganin cewa ana tafiya da zamani akan al-amura.

Da aka tambayi sarkin shin ko yana ganin diyar tashi zata iya gadon sarautar tashi, sai ya bayyana cewa, akwai al'ada da baza'a iya chanjata ba da kuma irin yanda mutane suka saba yin al-amuran rayuwa amma watakila wataran diyarshi ko jikarshi zata iya zama sarauniyar Kanon.

No comments:

Post a Comment