Thursday, 1 March 2018

Dubun matshin dake amfani da sunan Sarkin Kano a Instagram ya cika: An kamashi

Masu iya magana na cewa kwana dubu na barawo kwana da ya na me kaya, dubun matashin da ya bude dandalin yanar gizo a shafin Instagram da sunan me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ta cika, 'yan sanda sun yi ram dashi bayan bincike na tsawon lokaci.

Dandalin wanda yake da mabiya sama da dubu dari biyu kuma har shafin na Instagram ya tantanceshi a matsayin sahihin shafin me martaba sarkin Kano na saka hotuna da bayanai dake ikirarin cewa sarkin Kanone ya fada, a kawanakin baya shafin ya rika saka labarai da suka rika daukar hankula da zama kanun labari a jaridu da shafukan yanar gizo.
Wannan dalilin yasa me martaba Sarkin Kanon ya fito ya nesanta kanshi da wannan shafi inda yace bashi da shafin yanar gizo kuma be cewa kowa ya bude shafin yanar gizo da sunanshi ba, amma duk da wancan bayani da sarki yayi wasu basu ji ba.
Yaudai ga dubun matashin dake da shekaru ashirin da haihuwa a Duniya sun cika.

Wani abu da wasu mutane basu sani ba da yanar gizo shine: karka rika saka labarai hotuna ko kuma ka rika abubuwa da tunanin cewa wai ba'a sanka ba, ko kuma zaka goge nan gaba. Duk wani abu da ka saka a yanar gizo to ko da ka gogeshi akwai yanda za'a nemoshi ya dawo.

Wannan wani ilimine me zaman kanshi, saboda haka duk abinda baka so Duniya ta sani zaman lafiyar ka shine ka da ka sakashi a yanar gizo. Ko kuma ka rika amfani da sunan wani kana abinda kaga dama, duk taka tsantsan dinka akwai yanda za'a gano ka. Masu yin abinda suka ga dama a yanar gizo susha lallai suna da wani ilimine me zaman kashi ta yanda duk abinda suka yi sun san yadda zasu badda sahu koda anyi bincike ba za'a gano su ba kuma mafi yawan masu wannan ilimi suna kasashen Amurka, Rasha da Koriya, suma ba ko da yaushe suke shan lallai ba, wasu lokuta ana gano su. Allah ya kyauta.

No comments:

Post a Comment