Saturday, 17 March 2018

'Duk wanda ke sona dan wani to ya daina: Ya kamata a rika girmama Adam A. Zango'>>Genaral BMB

A cigaba da caccakar da yakewa Ali Nuhu, Bello Muhammad Bello, General BMB ya bayyana cewa tarin masoya da basu fada mishi gaskiya dan kada ranshi ya baci basu da amfani a gareshi dan haka gara 'yan kadan da zasu gayamai gaskiya, kuma ya bayyana cewa duk wani da yake sonshi tsakani da Allah ba dan wani Kato ba to dashi zai tafi. Amma duk me sonshi saboda wani jarumi to ya daina.


Haka kuma jarumin yayi kira ga masana'antar fina-finan Hausa da ta rika girmama Adam A. Zango dan shima yanzu ya zama babba a harkar, yayi kira na musamman ga na kusa da Ali Nuhu da su rika girmama Adam A. Zango inda yace tun Adamun yana Jos kaninshine yanzu kuma ya koma abokinshi kuma ya kai matsayin da za'a rika girmamashi a masana'antar.

Ya kara da cewa duk wanda ya sake taba Adam A. Zango bazai bari ba sai ya rama mishi domin shima yanzu ya zama babba.

Ali Nuhu dai har yanzu be tanka mishi ba.

No comments:

Post a Comment