Sunday, 11 March 2018

Fadakarwa akan munafurci daga Sheikh Isa Ali Pantami

Babban malamin addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami yayi fadakarwa akan munafurci, malamin ya fara da cewa, daya daga cikin mafi munin cutar dake lalata zuciya shine munafurci, munafukai sune mafiya hadarin mutane a wannan Duniyar. A koda yaushe suna kokarin kawo kiyayya da rudani a tsakanin mutane. Kayi kokarin kiyayarsu kuma kada ka kasance daya daga cikinsu.

 
Munafurci ciwone kuma lefine babba. Munafurci na nufin mutum ya bayyana gaskiya da kyawawan halaye a fili amma a zuciyarshi ya boye mugun hali da kafirci. Munafukai na jin dadin ganin sun hada mutanen dake zaune lafiya fada, su mayar dasu makiyan juna.
Babu hukuncin da ya fi wanda za a yiwa munafiki muni. Allah madaukakin sarki yace" Lallai munafukai zasu kasance a can karkashin kasan wuta: Ba su da mataimaki".
Alamu hudu da ake gane munafiki dasu, duk wanda ya hada wadannan alamu duka to cikakken munafikine, wanda kuma yake da wasu daga cikin wannan alamu to yana da burbushin munafurci a tattare dashi, har sai ya dena, ya tuba:

Idan yayi magana yayi karya.

Idan yayi alkawari ya saba.

Idan an bashi amana yaci.

Idan ana musu dashi sai ya koma yana zagi.

No comments:

Post a Comment