Sunday, 18 March 2018

Fadar shugaban kasa ta aika da tawaga jihar Bauchi dan mika sakon ta'aziyyar rasuwar sanata Ali Wakili

Gwamnatin tarayya ta tura tawaga ta musamman jihar Bauchi inda suka mika sakon ta'aziyyar fadar shugaban kasa ga al-ummar jihar na rashin sanata Ali Wakili da sukayi wanda ya rasu jiya sanadiyyar gajeruwar rashin lafiya.Tawagar wadda a ciki hadda shugaban ma'aikata, Abba Kyari sun kaiwa sarkin Bauchi da Gwamna ziyara inda suka mika ta'aziyyar fadar shugaban kasar.

Muna fatan Allah ya gafartawa sanata Ali Wakili.

No comments:

Post a Comment