Wednesday, 7 March 2018

Garin dadi na nesa: Likitocin kasar Canada sunki amincewa da karin albashin da aka musu saboda kudin sunyi yawa

A yayin da wani ke kokawa akan rashin wani abu na rayuwa, wani shi kuma na can abinnan ya isheshi harma neman kai yake dashi, irin haka ta faru a kasar Canada inda likitocin kasar sukayi zanga-zangar rashin amincewa  da karin albashin da aka musu.


Wannan wani abune dake nuna cewa suna sowa 'yan uwansu abinda suke soma kansu domin kuwa likitocin sun nuna kin amincewa da karin albashinne saboda ma'aikatan jiyya da marasa lafiya na cikin halin neman taimako, ba'a taimaka musu ba sai su kuma dake sama dasu aka kara musu albashi, wannan dalilin yasa sukace basu aminceba.

Likitocin su kusan dari biyar da wasu dalibai dake koyan aikin likitancin a kasar su kusan dari da hamsin sun sakawa takardar kin amincewa da karin albashin da aka musune sukace saidai idan za'a inganta yanayin aikin ma'aikatan jiyya da kuma na marasa lafiya sannan zasu amshi wannan karin albashi.

Wai lallai garin dadi na nesa.

No comments:

Post a Comment