Thursday, 22 March 2018

Gwamna Ganduje a gurin taron tattalin arzikin kasa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kenan a gurin taron tattalin arziki na kasa da akayi yau a Abuja inda aka tattauna batun yanda za'a samar da kwararrun mutanen da zasu rika yin ayyukan da suka dace a ma'aikatu daban-daban na kasarnan da samun habakar attalin arziki.


Hamshakan attajiran Duniya, Bill Gates da Aliko Dangote sun halarci wannan taro wanda mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo ya jagoranta.

Gwamna Ganduje ne a wannan hoton aka daukeshi yana gaisuwa hannu biyu-biyu a gurin taron.

No comments:

Post a Comment