Wednesday, 28 March 2018

Gwamnatin jihar Kano zata fara ginin gadar Dangi ranar litinin me zuwa

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa za'a fara aikin ginin gadar sama ta shataletalen Dangi dake kusa da titin Zoo ranar Litinin idan Allah ya kaimu, dan haka take sanar da masu amfani da ababen hawa da su yi amfani da wasu hanyoyi na daban dan magance samun cinkoson ababen hawan.


Zadai a gina gadarne akan tsabar kudi naira Biliyan hudu kamar yanda me baiwa gwamnan shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.


No comments:

Post a Comment