Sunday, 18 March 2018

Gwamnatin jihar Kebbi ta aurar da zawarawa 100

Gwamnatin jihar Kebbi karkashin gwamna Atiku Bagudu ta aurar da zawarawa dari da kuma yi musu kayan daki da kudinsu ya zarta dubu dari da hamsin kowacce haka kuma an baiwa matan kudi dubu talatin-talatin dan su kama sana'a.


An daura auren a fadar sarkin Argungun, me martana Isma'ila Mera, kamar yanda jaridar Leadership ta ruwaito, kuma malaman addini da suka hada da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Sheikh Masur Sakkwato da sauransu sun halarci gurin taron.

A wani sako daya fitar ta dandalinshi na sada zumunta, Sheikh Amimu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa an daura auren zawarawan babu badala ko mi an yishi bisa sunna kuma sun yiwa amaren huduba me kyau.

Ga abinda ya fada kamar haka:

"TARON AURE ZAWARAWA DARI

TARO MAI ALBARKA A KASAR ARGUNGU TA
 JIHAR KEBBI
AN AURAR DA ZAWARAWA GUDA DARI
ANYI MUSU SHA TARA TA ARZIKI
GANI TARE DA SARKIN KABIN ARGUNGU
DA CHAIRMAN.
DR MANSUR IBRAHIM SOKOTO
DR NAZIFI INUWA KANO
ALARAMMA AHMAD SULAIMAN KANO 
GURI YA CIKA MAKIL
MUNYIWA AMARE DA ANGWAYE, NASIHA KUMA ANYI KOMAI AKAN SUNNAH BABU BADALA, KO FITSARA
ALLAH YASA ALBARKA"

No comments:

Post a Comment