Wednesday, 7 March 2018

Hadimar Masallacin Sultan Bello Dake Kaduna Ta Rasu

Innalillahi Wa Inna ilaihir raji'un!! 

Mun samu labarin rasuwar Hajiya Hauwa'u wacce aka fi sani da suna Baba Mai Kayan Kamshi, wacce ta lashe shekaru da dama tana yi wa Masallacin Sultan Bello dake Kaduna hidima ta hanyar sanya turaren wuta a Masallacin domin ya yi kamshi, kuma ta dade tana yi wa Masallacin hidima tun zamanin Marigayi Malam Abubakar Gumi.


Tuni dai aka yi jana'izar ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. 

Babah yadda kika sadaukar da rayuwarki wajen sanya kamshi a Dakin Allah, Allah muke roko ya sanya kamshi cikin kabarin ki, ya sanya Aljanna ce makomarki. Allahumma Amin.
Rariya

No comments:

Post a Comment