Thursday, 8 March 2018

Hadiza Gabon ta bayyana wanda ya koya mata sosayya

Da alama dai tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon tana cikin soyayya da wani tsundum kuma ta kamu sosai, domin kwanannan sai kalamai take yi dake nuna hakan, a makon daya gabatane Hadizar tayi amfani da hoton Hassan Giggs da matarshi Muhibbat Abdulssalam inda ta cewa masoyin nata ya kula irin soyayyar da take so su rikayi dashi kenan.


To a yanzu ma Hadizar ta sake bayyana cewa ta dalilin masoyin nata tasan me ake cewa soyayya, saidai har yanzu taki fitowa ta bayyana ko wanene.

A kwanakin bayane dai wani masoyin Hadizar wanda ya nuna da gaske yake da suka hadu a dandalin Twitter yayi ta naci har sai da ya samu lambarta, to ko shi dinne ko kuwa wanine?

Koma dai menene, lokaci be bar komaiba, muna musu fatan alheri.

No comments:

Post a Comment