Wednesday, 21 March 2018

Hoto me birgewa: Yanda uwa ke rubuta jarabawa rike da diyarta

Allah sarki wannan wata uwace a kasar Afganistan dake rubuta jarabawar shiga Jami'a sai diyarta ta fashe da kuka, ta tashi ta amsota daga hannun wadda take rike da ita, sai tayi shiru, me kula da rubuta jarabawar yace ganin haka ya kyale ta ta rike diyartata a lokaci guda kuma tana rubuta jarabawar, inda ta samu bayan wata kujera ta zauna.Ya kara da cewa abin ya birgeshi shine ya kasa jurewa sai da ya dauketa hoto.

Allah ya sakawa iyayenmu da Alheri.

No comments:

Post a Comment