Sunday, 18 March 2018

Hukmar 'yan sanda ta karyata cewa shugaba Buhari ya matsi shugaban hukumar akan rashin biyayyar da yayi mishi

Hukumar 'yan sanda ta hannun mataimakin kwamishina kuma me magana da yawun hukumar Jimo moshood ta karyata cewa wai shugaba Buhari ya matsi shugaban 'yan sanda, Ibrahim Idris akan dalilin barin jihar Benue da yayi bayan da shugaba Buharin ya bashi umarnin komawa jihar da zama dan magance rikicin dake faruwa a can.


Da yake shaidawa jaridar Thisday abinda ya Faru, Moshood yace shugaban kasa be matsi shugaban 'yan sandan ba akan wancan lamari kuma idan akwai wanda yace hakan ya faru to ya fito da takardar tambayar da shugaba Buharin ya yiwa shugaban 'yan sandan Duniya ta gani.

A ziyarar da shugaba Buhari yakai jihar Benue ne dan jajintawa al-ummar jihar akan rikicin da ya faru wanda yayi sanadiyyar asarar rayuka, gwamnan jihar da sauran shuwagabannin al-umma suka shaida mishi cewa shugaban 'yan sandan be taba kwana a jihar ta Benue ba tunda ya turoshi, rana da ya kawai yaje ya wuce jihar Nasarawa, shugaba Buhari ya nuna mamaki akan wannan lamari inda yace besan cewa shugaban 'yan sandan bebi umarnin daya bashi ba.

Bayan komawar shugaba Buhari Abuja, wakilan fadar Aso Rock sun shaidawa Duniya cewa shugaba Buharin ya matsi shugaban 'yan sanda akan rashin biyayyar da ya mishi, to amma yanzu hukumar 'yan sandan ta karyata haka.

No comments:

Post a Comment