Wednesday, 28 March 2018

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sammacen kama Sanata Dino Melaye ga 'yan sandan kasa da kasa

Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce ta ankarar da hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa watau INTERPOL cewa ta kama dan majalisar dattawan kasar Sanata Dino Melaye da wasu mutane bakwai.


A ranar Laraba ne dai aka tsara cewa dan majalisar da kuma sauran mutanen bakwai za su gurfana gaban wata kotu da ke jihar Kogi bisa tuhumarsu da hannun a wasu ayyukkan kisa da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane amma sai ba su bayyana ba.

Sai dai babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim K. Idris, ya sauke kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi, CP Ali Janga daga kan mukaminsa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar Jimoh Moshood ya aikewa manema labarai ta ce, an sauke shi ne saboda guduwar mutum shidan da aka tsare da su.

Sanarwar ta kuma ce ana tsare da wasu jami'an yan sanda 13 kuma ana bincike a kansu dangane da rawar da suka taka a guduwar mutanen su shida.

Babban sufeton 'yan sanda ya umurci CP Esa Sunday Ogbu ya wuce jihar Kogi kuma ya fara aiki a matsayin kwamishinan yan sanda na jihar.

Ibrahim Idris ya tura da tawagar kwararu masu bincike zuwa jihar kuma tuni suka isa garin Lokoja domin su sake kama wadanda suka tsere.

Hukumar 'yan sanda ta ce mutun shiddan da suka tsare tun farko sun bayar da shaidar cewa dan majalisar dattawan kasar Dino Melaye yana goyon bayan 'yan fashi da makami suka yi.

Sai dai a hirar da ya yi BBC a baya-baya nan Sanata Melaye ya musanta zargin.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment