Saturday, 10 March 2018

'Idan aka baiwa mata karin dama a cikin harkar gwamnati zasu iya yiwa maza juyin mulki>>Gudaji Kazaure

Wani bidiyon dan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure yana magana akan baiwa mata karin dama akan harkar gwamnati ya dauki hankulan mutane sosai, dan majalisar yayi kira da cewa ayi hankalifa kada a baiwa mata karfi sosai a cikin harkar mulki, domin suna da wayau sosai.


Ya bada misalin cewa, mata su ke kula da yara a gida suna girka abinci kuma zaka ga babban mutum a waje amma matarshi na juyashi a cikin gida , ya kara da cewa da yawa idan kana neman wani abu a gurin wani babban mutum idan kabi ta hanyar matarshi kafi samun abin cikin sauki, dan haka yace irin wannan karfi da mata ke dashi akan maza idan aka basu karin damar shiga harkokin gwamnati zasu iya yiwa maza juyin mulki.

No comments:

Post a Comment