Monday, 19 March 2018

'Idan kana da wata Diyar da bakawa aure ba ka bani: Ni zan zama matar ita ta zama mijin>>Wani ya gayawa Dangote

Bayan da aka sha shagalin bikin diyar hamshakin attajirin Duniya, Fatima Aliko Dangote da angonta Jamil MD Abubakar, wani bawan Allah ya gayawa Dangoten ta dandalinshi na sada zumunta da Muhawara cewa idan yana da wata 'yar ya bashi.

Bawan Allahn ya kara da cewa idan Dangoten ya bashi auren shi zai zama matar ita ta zama  mijin, zai rika girki, shara, da kulda da yara ita kuma taje ta nemo Kudin.

Wannan roko da wannan bawan Allah yayi yaja hankulan mutane.

No comments:

Post a Comment