Tuesday, 27 March 2018

'Ina alfahari da kasancewata 'yar Afrika'>>Ummi Zeezee

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee tayi wani bayani akan manyan harsunan Duniya, inda tace, yaren Larabci yafi kowane yare dadin saurare, sannan yaren Indiyanci yafi kowane yare dadin yin waka, sannan yaren turanci yafi kowane yare lakwasa harshe wajan yinshi sai kuma yaren Chainanci wanda yafi kowane yare wahalar magana.


Tace amma bakin mutum dan Afrika shi kuma yafi kowa iya koyan kowane yare cikin sauki yanda zaka ji kamar nashi, Ummi ta kara da cewa tana alfahari da kasance warta 'yar Afrika.

"Larabci,yafi ko wani yare dadi a wajen maganah"indiyanci,yafi ko wani yare dadi a wajen waka”turanci yafi ko wani yare lankwasa harshe a wajen maganah”chainanci yafi ko wani yare wuya a wajen maganah”bakin mutum kuma yafi kowani yare wajen saurin fahimtar yaren da ba nashi ba a karamin lokaci,dan zaka iya ganin bakin mutum yana indianci sosai ba mistake aciki sai kace yarensa .#MASHAA ALLAH AM SO PROUD TO BE AFRICAN".

No comments:

Post a Comment