Tuesday, 20 March 2018

Ina fadin cewa ni nafi kowa a Duniyar kwallo kuma ina tabbatar da hakan a aikace

Kasar Portugal ta bayyana Cristiano Ronaldo a matsayin gwarzon dan kwallon kasar na shekarar 2017 data gabata, da yake jawabi akan wannan kyauta da ya samu yace kyautace a gareshi da abokan aikinshi gaba daya.


Haka kuma ya kara yin baki kamar yanda ya saba da cewa, a koda yaushe yakan fadi cewa shine yafi kowa a Duniyar kwallo kuma yana tabbatar da hakan a aikace idan yana buga wasa.

No comments:

Post a Comment