Sunday, 25 March 2018

Jami'an tsarone ke goyawa masu kashe 'yan Najeriya baya>>T. Y Danjuma

Tsohon ministan tsaro T. Y Danjuma yayi kira ga 'yan Najeriya da su tashi tsaye su kare kansu bisa irin hare-haren da 'yan ta'adda suke kai musu musamman a jihar Taraba inda ake samun hare-haren fulani makiyaya, yace jami'an tsarone ke goyawa maharan baya.


Danjuma yayi wannan jawabine a gurin wani taron yaye daliban jami'ar jihar da akayi a Jalingo inda ya kara da cewa idan mutane suka tsaya dogara da jami'an tsaro to kuwa za'a kashe su.

Yayi zargin cewa wannan kashe-kashen wani yunkurine na kawar da wata kabila daga doron kasa wanda wasu suka shirya. wannan batu dai ya dauki hankulan mutane inda ake ganin babban mutum a kasarnan irin T. Y Danjuma be kamata yayi wannan furuciba.

No comments:

Post a Comment